Tsoffin Kansiloli Sun Ba Gwamna Fintiri Bus Siana Hudu

Tsoffin Kansiloli Sun Ba Gwamna Fintiri Bus Siana Hudu

Tsoffin Kansiloli Sun Ba Gwamna Fintiri Bus Siana Hudu

 Kungiyar tsoffin kansilolin jihar Adamawa ta baiwa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri tallafin motocin kirar Siana guda hudu

 An samar da motocin ne a matsayin wani bangare na kayan aiki don bunkasa yakin neman zaben Gwamna Fintiri.

Tsoffin Kansiloli Sun Ba Gwamna Fintiri Bus Siana Hudu

 Shugabannin kungiyar,l Micheal Okopi da Malam Suleiman ne suka gabatar da motocin a ranar Talata a gidan gwamnati na Yola.

 Sun sha alwashin hada kai da Gwamna Fintiri da sauran ‘yan takarar jam’iyyar PDP goyon baya a zaben 2023.

 Gwamna Umaru Fintiri wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya Farfesa Maxwell Gidado ya yaba da tallafin.

 Ya kuma yi kira ga tsaffin kansilolin da su hada kan jama’ar su domin tabbatar da nasarar jam’iyyar PDP a zaben badi.

Post a Comment

0 Comments