Amfanin cin Fara ga Lafiyar Jikin Dan Adam

Amfanin cin Fara ga Lafiyar Jikin Dan Adam


 Fara na daga cikin dangin kwari, amma duk da haka, cin ta na da amfani ga jikin dan Adam kamar sauran dabbobi.

Wani bincike ya nuna cewar Duk itacen da Rakumi ke ci Fara ma na ci a don haka amfanin da Nonon Rakumi ke yi wajen warkar da cutuka ita ma Fara ta na dauke da Sinadarin a jikinta.

A kasarmu NAJERIYA ana cin farar sosai ta yadda har wasu sun dauketa matsayin abin marmari da kusan kowa ke ci.

Akan soya farar kamar yadda ake soya nama, amma sai an fara tafasa ta kafin a zuba kayan hadi sannan a soye ta.

Fara na dauke da sinadaran vitamin A, B da D, wadanda duk su na taka muhimmiyar rawa wajen gina jiki.

Haka kuma fara na dauke da sinadarin Protein wanda yawansa har ya fi wanda ya ke cikin kifi da nama.

Wani babban likita ya tabbatar cewa fara na dauke da kashi 62.93 cikin 100 na sinadarin Protein wanda kashi 89.63 cikin 100 dinsa ke bin lafiyar jiki.

Har ila yau fara na dauke da sinadaran calcium, magnesium da zinc wadanda ke taka muhimmiyar rawa wajen gina kashi.

Post a Comment

0 Comments