Amfanin Kankana Ga Lafiyar Dan Adam

Amfanin Kankana Ga Lafiyar Dan Adam


 Hausawa na yiwa kankana kirari da cewa Kankana uwar ruwa, ba komai ya sa ake yiwa kankana wannan kirari ba sai don masana sun ce kusan kashi 90 cikin dari nata ruwa ne.

A wannan makala muna fatan kawo alfanun kankana ga lafiyar dan adam, sannan da yin tsokaci akan cututtukan da take magani da kuma riga-kafi.

 

Kafin bayyana amfanin kankana garemu zai fi kyau mu sani idan ana son samun cikakkiyar fa’idaeta, to lalle a yi amfani da wacce  ta nuna sosai don masana sun ce sinadaran nunanniyar ya fi taruwa sosai musamman “beta-carotene” dake cunkushe a cikin jar tsokar nan wanda ke da matukar amfani wajen kara karfin ido.

Hakanan kamar yadda muka ce tun da farko kashi 90 cikin dari na kankana duk ruwa ne don haka tana taimakawa jiki samun isasshen ruwa.

Kar dai mu kai ku da nisa kankana ta tara fa’idoji masu yawan gaske da suka hada da karin kuzari ga da namiji yayin jima’i, gyaran fata musamman ga mata, riga-kafin cututtuka zuciya, rage hawan jini, samar da karfin  jiki, da sauran fa’idoji.

Post a Comment

0 Comments