Amfanin Man Alayyadi Guda Goma Sha Daya(11) Ga Lafiyar Dan-adam

Amfanin Man Alayyadi Guda Goma Sha Daya(11) Ga Lafiyar Dan-adam


 Al’ummar kasar Maroko sun kasance su na amfani da Man alayyadi shekaru aru-aru da suka gabata – ba wai kawai saboda maikonsa, ko kara dandanon abinci ba, sai dai saboda  fa’idodin kiwon lafiya da yawa da Man alayyadi ke dauke da su.

Ana samun man alayyadi daga ‘ya’yan bishiyar “Argan” a turance,  kuma su ‘ya’yan wanan bishiya sun yi kama da ‘ya’yan kwakwar man ja da muke da ita a kudancin wannan kasa ta mu. Hakanan, ana kira man alayyadi da “Argan Oil” da turanci.

Ko da yake asalin bishiyar “Argan” ko kuma shi man alayyadi Æ™asar Maroko ne, amma a yanzu ana amfani da man alayyadi a duk faÉ—in duniya don dafa abinci iri-iri, kayan kwalliya da kuma magani.

Saboda matukar muhimmmanci da man alayyadi ke da shi ga lafiyar al’umma, Mujalla ta yi dogon nazari da bincike, inda daga karshe mu ka gano amfanin man alayyadi guda goma sha daya (11) ga lafiyar Dan- adam.

1. Man Alayyadi Ya Kunshi Mahimman Sanadirai Masu Gina Jiki

Da farko Man alayyadi ya ƙunshi fatty acids da kuma sanadarin phenolic mai yawa, wadanda sanadarai dake kan gaba wajen samar wa jiki koshin lafiya .

Kusan 29-36% na sanadaran fatty acid dake kunshe cikin man alayyadi ya samuwa ne daga linoleic acid, ko omega-6, inda ya ke juya shi zuwa kyakyawan mai  dake samar da nau’ikan sandarai ma su gina jiki.

Oleic acid, ko da yake ba shi da mahimmanci, yana da Kashi 43-49% na fatty acid, amma irin wannan sanadari dake ciki man alayyadi kuma yana da lafiya sosai.

Ana iya samun wannan snadari a cikin man zaitun kuma, oleic acid ya shahara saboda ingantaccen tasirin sa akan lafiyar zuciya.

Bugu da ƙari, masana na sanya man alayyadi a cikin jerin mayukan da ake ganin sune tushen bitamin E, wanda ake buƙata don lafiyar fata, gashi da idanu. Wannan bitamin kuma yana tattare da sandaran antioxidant masu yawan gaske.

2. Man Alayyadi ya Na Kara Lafiyar Zuciya

Man Alayyadi shine tushen sanadaran oleic acid, wanda shine kitse mai kunshe da omega-9 fatty acid.

Hakanan ana samun Oleic acid a cikin man alayyadi baya ga samun irin wannan sanadari a wasu nau’ikan abinci da yawa, kamar avocado da man zaitun, kuma galibi ana danganta shi wannan sanadari da tasirin wajen bai wa zuciya kariyar daga kamuwa daga cututtuka .

3. Man Alayyadi Na Bada Kariyar Kamuwa Da Ciwon Suga

Wasu binciken baya-bayan nan da masana suka gudanar ya nuna cewa, amfani da man alayyadi  na iya taimakawa wajen hana kamuwa da ciwon suga.

4. Man Alayyadi Na Bada Kariyar Kamuwa Da Ciwon Daji

Man Alayyadi na iya jinkirta ko hana girma wasu nau’ika na Æ™wayoyin cutar ciwon daji wato “Cancer”.

5. Man Alayyadi Na Kara Inganta Lafiyar Fata

Man alayyadi ya shahara kwarai da gaske wajen inganta lafiyar fata, inda ya ke rage alamun tsufa ga fata.

6. Man Alayyadi Na Iya Magance Wasu Cututtukan Fata

Man Alayyadi ya kasance sanannen maganin da ake amfani da shi a gida ko ta hanyar gargajiya don magance wasu cututtukan fata kamar kumburi, shekaru da yawa da su ka gabata ,musamman a kasashen dake yankin Arewacin nahiyar Afirka, inda daga nan ne bishiyoyin “argan” da ake samun man alayyadi ta samo asali.

7. Man Alayyadi Na Iya Saurin Warkar Rauni

Binciken da aka gudanar a baya-bayannan ya nuna cewa, ko shakka babu Man alayyadi ya na taimakawa wajen hanzarta warkar da rauni.

8. Man Alayyadi Na Kara Laushi Da Kyan Fata da Gashi

Sanadaran Oleic da linoleic waɗanda suke ƙunshe mai alayyadi sune mahimman sanadaran gina jiki don inganta lafiyar fata da gashi.

9. Ana Amfani Da Man Alayyadi Don Maganin Kurajen Fuska

Wasu nazarce-nazarce da bincke sun tabbatar da tasirin man alayyadi a matsayin magani mai mahimmanci wajen warkar da kurajen fuska.

10. Man Alayyadi Na Kara Karfin Garkuwar Jiki

Wani bincike da aka gudanar kuma aka wallafa a wata Mujallar lura da lafiya ta bayyana yadda man alayyadi ke inganta wa tare da kara karfin garkuwar jikin dan-adam. Wannan kuwa yana da nasaba ne da wasu muhimman sanadarai da man alayyadin ya ke kunshe da su.

11. Man Alayyadi Na Warkar Da Ciwon Daji Na Fata.

Mun bayyana a wannan makala a sama cewa, man alayyadi na bada rigakafin kamuwa da wasu daga cikin nau’ika cutar daji. Haka kuma ya na maganin cutar daji da ta riga ta kama fata.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Post a Comment

0 Comments