Bayyanar Wannan Halitta A Cikin Jama’a Ya Dauki Hankalin Al’umma

Bayyanar Wannan Halitta A Cikin Jama’a Ya Dauki Hankalin Al’umma


 Subhalallah: Bayyanar Wannan Halitta A Cikin Jama’a Ya Tada Hankalin Al’umma, Idan Bakada Tsoro 

~Blood Waterfall! Ɓulɓulowar Jini Daga Kan Dutse!

 

Antarctica daya daga cikin continent ne guda bakwai da muke dasu a duniya, amma tana da abin al’ajabi da mamaki, wanda har yau masana kimiyya basu gano su ba.

 

Kashi casa’in da tara (99%) na Antarctica kankara ne, da sanyi mai tsanani, kashi daya (1%) ne kaɗai busashshen wuri (dry land). Karkashin wannan kankaran mai girma, akwai sirruka dayawa da ba’a gano su ba, wasu daga cikin masana suna riya cewa akwai yiwuwar wani gari ne mai girma mai suna Atlanta aka birne karkashin kankaran, wanda suke kira da turanci “The Lost City Of Atlantic”.

 

Kuma wani abin mamaki shine, ɓulɓular ruwan jini daga duwatsun kankara, wanda suke zubowa kamar waterfall, Kuma duk da sanyin da akeyi a wurin, wannan ruwan jinin bai daskare ba! Lallai akwai darasi anan ga masu tunani. Da kuma wasu dabbobi wanda halittu ne daban da wanda muka saba gani. Wasu akan cikunansu suke tafiya, kamar yadda Allah Yace; “Kuma Allah ne Ya halitta kõwace dabba daga ruwa. To, daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya a kan cikinsu…” (An-Noor:45)

 

Hakika Allah Yayi kira garemu acikin Al-Qurani dacewa; “Shin, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasa, dõmin su gani yadda ãƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Allah Ya darkãke a kansu. Kuma akwai misãlan wannan ãƙibar ga kãfirai (na kõwane zãmani).” (Muhammad:10)

 

Idan dai ta tabbata akwai wasu waɗanda aka halaka a karkashin dutsen kankaran nan, to tabbas waɗan nan sun ɗanɗana azaba mai raɗaɗi, kuma darasi ne garemu, wannan iko ne daga cikin ikon Allah.

 

أَفَلَمْ يَسِيرُوا فِي الْأَرْضِ فَتَكُونَ لَهُمْ قُلُوبٌ يَعْقِلُونَ بِهَا أَوْ آذَانٌ يَسْمَعُونَ بِهَا ۖ فَإِنَّهَا لَا تَعْمَى الْأَبْصَارُ وَلَٰكِن تَعْمَى الْقُلُوبُ الَّتِي فِي الصُّدُورِ

 

Ita labarin “Atlanta” ko ince “Lost City Of Atlantic” ta samo asali ne daga wani ɗan falsafa da ake kira Plato. Ya bada labarin ne a shekarar 360 B.C. Ya bada labarin ne da cewa, kasar Atlantar ta kasance ta kware wojen yaki akan ruwa, tana da arziki, da zinari, kuma suna rayuwa ne akan sibiri, daula ne mai tsananin karfi da girma, tana aikata fasadi da ɓarna a doron kasa, sai Ubangijinsu ya halaka su ta hanyar nutsarwa. Idan wannan labarin ta tabbata, to mu dai munsan Allah ne ya dammara su, saboda zunubansu, kuma yabar aya ga mu da muka zo bayansu.

 

«Ku duba karkashin ɗaya daga cikin hotunan nan nayi ɗan karin bayani, gameda jan ruwan dake ɓulɓulowa daga dutsen»

 

Allah Ya tsare mu, Ya sa mu kyautata tamu rayuwar, ta yadda duniyar mu, da lahirar mu, bazata zame mana nadama ko da nasani ba. Aameeen.

Post a Comment

0 Comments