Nuhu Abdullahi Yayi Martani Ga Masu Cewa Shi Ya Ingiza Nafisa Abdullahi Ta Fita Daga Shirin Labarina

Jarumi Nuhu Abdullahi Wato Mahmud A Cikin Shirin Labarina. Yayi Bayani Game Da Mutanen Dake Cewa Shiya Ziga Nafisa Itama Ta Fita Daga Shirin Labarina Series.

Jarumin Ya Sami Bada Amsar Ne A Kujerar Gabon Talk Show, Inda Ya Halarci Shirye Shiryen Da Hadiza Gabon Ke Gabatarwa. Hadiza Gabon Din Tayiwa Nuhu Abdullahi Tambayoyi Da Dama, Inda Shima Ya Bata Amsa Dai Dai Irin Tambayoyin Data Mishi.

Idan Baku Manta Ba, Kusan Lokaci Guda Akaga Nafisa Abdullahi (Sumayya) Tare Da Nuhu Abdullahi (Mahmud) Su Yanke Alakarsu Da Kamfanin Saira Movies, Inda Hakan Yasa Su Futa Daga Cikin Shirin Na Labarina, Fitasu Daga Shirin Yasa Mutane Su Dinga Cece Ku Ce.

Kan Cewa Ana Ganin Kamar Nuhu Abdullahi Shi Ya Hurewa Nafisa Abdullahi Kunne Domin Itama Ta Fita Daga Shirin Bayan Shi Ya Fara Ficewa.

Post a Comment

0 Comments