Shin Kokasan Mashimmancim Giginya Ajikin Dan Adam

Shin Kokasan Mashimmancim Giginya Ajikin Dan Adam


 1 – doddoya (Scent Leaf): Wannan ganye da aka fi sa wa ko a miya ko a dafa-duka domin karin kamshin abinci, yana da matukar amfani ga lafiya. Binciken masana kayan abinci da na ganyaye da dama bai nuna illar wannan ganye ba ga lafiya, sai dai ma nuni ga alfanun da zai iya yi wa mutane masu farfadiya da hawan jini.

2 – dinya (Black Plum): Wasu ’ya’yan itatuwa ne da mukan sha a yau-da-kullum. dinya na daya daga cikin albarkatun itatuwa da Allah Ya yi mana a wannan kasa, wadda kusan muka kusa mantawa da ita. Tana da sinadaran bitaman musamman na rukunin C da ma’adinai irinsu potassium da dama, wadanda jiki kan bukata a yau da kullum. Tana da amfani wajen ware ciki kamar lemon bawo, ga wanda cikinsa ya cushe ya kasa bayan gida na tsawon kwanaki.

3 – dorawa (Honey Locust): Ita ma kayan marmari ce mai cike da amfani. Banda sinadarin fibre mai wanke ciki da tsane maikon da ke jikin hanji, an yi amanna wannan itace ’ya’yansa na da sinadarin protein irin wanda ake samu a gyada ko waken soya, wato bayan kayan marmari ke nan zai iya zama abinci.

4 – Gujiya (Bambara Nut): Wannan abinci da a da yake da yawa a kasar Hausa ta Najeriya, a yanzu wai a kasar Mali da Nijar aka fi noma shi. Kowa ya san dadi da gardin gujiya kamar na wake, amma ba ta kumbura ciki sosai kamar waken, kuma tana da gardin gyada har ila yau amma ba ta da maiko sosai kamar gyada. Kuma a kimiyyance dukan amfanin da ake samu a jikin wake da gyada, su gujiya ta hada a wuri guda. Lallai garin dadi na nesa.

5 – Goruba (Doum Palm): Wannan abinci mai cike da sinadarin fibre mai wanke cusasshen ciki da tsane maikon jiki, dusarsa kamar dusar aya amfaninsa yake, amma ya fi aya aiki. Akan iya fasa wadda ba ta nuna ba ma sosai a sha ruwanta kamar ruwan kwakwa. Masu bincike a kan wannan dan itace suna ganin idan ana cinsa za a iya rage hadarin kamuwa da ciwon hawan jini da na kiba.

6 – Kadanya (Shea): Su kuma ’ya’yan wannan itace maiko ne da su da wasu ke amfani da shi ba ma kawai a abinci ba, har da man shafawa da sabulu. Duka yawanci kayan marmari masu maiko suna da sinadaran bitaman da ake samu daga maikon ’ya’yan itatuwa, wato bitaman na rukunin A, D, E da K, dukkansu sukan hadu su gyara fata. Kai an tabbatar cewa ma wasu manya-manyan kamfanonin kayan shafe-shafen mai, man kade suke amfani da shi wajen hada mai, kamar yadda ake yi da man cocoa.

7 – Kabewa (Pumpkin): A da ba a yin miyar taushe ba tare da kabewa ba amma yanzu ’yan zamani sun rage sanya ta a miyar taushe. Ban da zaki da take kara wa miya, ita ce kadai a cikin kayan miyan da ke da sinadari mai gina jiki na protein, ga wadanda ba su samu sun sa nama ko kaza ba a miyar taushen. Bayan haka Allah Ya albarkace ta da sinadaran bitaman na rukunin A da na C. ’Ya’yan cikinta kuma wato agushi ba su da wadannan sinadaran bitaman amma suna da na protein sosai fiye da na ita kabewar da kuma sinadaran maiko irin na gyada, irin wanda jiki ya fi so.

8 – ’Ya’yan Kalaba ko Kuka (Baobab Fruit): Ko kuma ’ya’yan kuka wadanda a da ake yawan jikawa a yi lamurjensu ko kuma a rika tsotsa haka, suna da sinadarin bitaman na rukunin C kusan fiye da kowane ’ya’yan itace. A yanzu dai wasu kamfanonin yin abinci kamar masu yin zumar ‘jam’ ta biredi, sukan sa wannan kalabar a matsayin abin da zai sa danko.

9 – Kurna (Ziziphus): Binciken wasu masana a kasashen Sweden da Masar ya nuna cewa ’ya’yan kurna suna da sinadarai na ma’adinan calcium da potassium da magnesium. Yana da kyau mu ma a samu tsangayar da za ta yi bincike sosai a kanta a kasar nan. Sun kara da cewa a nan gaba suna ganin dole a yi bincike a kan yadda sukan iya kasha kwayoyin cuta da dama.

10 – Lansir (Cress): Wannan kayan lambu su kuma kusan suna da duk wani bitaman da jiki ke bukata amma na rukunin A da K da C sun fi yawa. Ga sinadarai na ma’adinai iri-iri duk a dan wannan ganye.

11 – Ridi/Kantu (Sesame Seed): Su ma wadansu ’ya’yan itatuwa ne masu matukar amfani ga lafiya. Bayan sinadaran bitaman da na ma’adinai irinsu iron, magnesium da calcium, yana da sinadarin protein mai gina jiki ga maiko kamar dai gyada, amma kusan ya fi gyada amfani saboda sinadari ko ma’adinin iron wanda jiki ke amfani da shi wajen sarrafa sabbin ’ya’yan jini.

12 – Rinji (Senna): Wannan wani ganye ne a cikin maganin da muke saya a kyamis mai sakin cusasshen ciki na dulcolad. Don haka amfaninsa yana da matukar tasiri ga masu matsalar taurin bayan gida. Sai dai idan aka yi amfani da shi da yawa zai iya sakin cikin sosai.

Post a Comment

0 Comments