Subahanallahi Kalli Yadda Wasu Yan Yawan Bude Ido Suka Gamu Da Naman Daji

Subahanallahi Kalli Yadda Wasu Yan Yawan Bude Ido Suka Gamu Da Naman Daji


 Subahanallahi Kalli Yadda Wasu Yan Yawan Bude Ido Suka Gamu Da Naman Daji

ANA CUTAR TALAKAN NIGERIA

Har yanzu bakuna sunki su saki sabbin kudade duk da CBN tace ta raba wa Bankunan sabbin kudaden, idan kaje ATM machine zaka cire kudi tsoffi zaka karba

Wasu ‘yan kasuwa sun fara kin karban tsoffin kudi saboda ganin wa’adin karban kudin ya kusa karewa suna tsoron karba, talaka na son ya sayi abinci babu hali

Wasu gidajen sayar da man fetur sun fara kin karban tsoffin kudi, hakan ya haddasa mummunan cutarwa ga masu ababen hawa da dogon layi

Wadanda suka kai kudinsu bankuna sun hadu da dogon layi, kowa ya ji a jikinsa saboda Bankuna basuyi tsari mai kyau ba, gashi yau saura kwana 8 wa’adi ya cika

Mutanen kauyuka basu da inda zasu je su canza kudaden su, mafi akasarin kananan hukumomin Nigeria basu da bankuna, sai sun biya kudin mota sun shigo birane inda akwai bakuna, gashi zasu tarar da dogon layi 

Wai CBN suna son cashless policy a koma online transactions ba tare da sunyi la’akari da cewa mafi akasarin talaka basa rike da smart phone ba, sannan har yanzu akwai inda babu service a kauyuka balle su sami access to internet, musamman yankin mu na Arewa sai munfi sauran yankin cutuwa

Hon Muhammad Gudaji Kazaure yace Gwamnan Babban Bankin Nigeria Godwin Emefele ya fito da batun canza fasalin kudi ne don a karkatar da mummunan satar da akayi a CBN, kuma babu wani kudi da aka canza fasali, tsofin kudade ne aka canza musu fenti, Hon Gudaji Kazaure yana son ganin Shugaba Buhari ya masa bayani amma tsinannu maciya amana sun toshe hanyar

Jama’a mu bi duk hanyar da ta dace mu tabbatar APC bata zarce da mulki ba, babu alheri a tsarin mulkin APC sharrin yafi yawa Wallahi, taron jam’iyyar maciya amana ne, sunci amanar Shugaba Buhari kuma sunci amanar ‘yan Nigeria

Tabbas da suna da imani da tausayi da sun hakura da wannan tsarin, ko kuma da sun kara wa’adi kamar nan da shekara 2, wannan tsarin talakawa kawai za’a cutar, manyan barayin Gwamnati da ake son a kama tuntuni sun dena ajiye madaran kudi, gwala-gwalai suke saya da kudin sata su boye

Allah Ka isar mana daga sharrin azzalumai ma­ciya amanar Nigeria

Post a Comment

0 Comments