YANDA ZA’AYI AMFANI DA DANKALIN TURAWA (POTATOES) DOMIN RABUWA DA KURAJEN FUSKA

YANDA ZA’AYI AMFANI DA DANKALIN TURAWA (POTATOES) DOMIN RABUWA DA KURAJEN FUSKA


 Assalamu Alaykum,

Dafatan kowa yana cikin koshin lafiya.

Mun sani lallai za’a samu wasu su fara yin mamaki ta yaya hakan sai kasance, abinda ake ci ace shine kuma za’a shafa a fuska domin maganin kuraje.

Eh hakana kada ayi mamaki abisa wani bincike da akayi angano cewa lallai yin amfani da dankalin turawa a fuska ko ajiki yana magance matsalar kuraje da fata.

Abinda ake bikata kawai shine,
A samu dankalin daidai gwargwado sai a wanke domin a rabashi da datti.

Sannan sai a fere a cire bawon duka,
Bayan haka sai a zubashi acikin blanda a markade a dan zuba ruwa dan kadan, idan babu blanda ana iya amfani da magurji (grater) a gurje, idan an kammala sai a juye a wani mazubi mai kyau, ana iya zuba zuma aciki a gauraya.

Sai a diba a shafa a fuska kamar yadda zaku gani a cikin hoton, ko a shafa inda ake bukata a jiki.

A shawarce yana da kyau a shafa kafin a kwanta bacci, sai a barshi a fuska har tsawon minti 30–40,.

A wannan lokacinne za’aji ya kama fuska sosai ya fara bushewa.

Daga nan sai a wanke da ruwan dumi,
Ana son ayi haka kullum har tsawon kwanaki bakwai za’a ga kyakkyawan sakamako da izinin ubangiji.
Allah yasa a dace.

Dankalin Turawa 🥔🥔yana cikin amfanin gona ne mai son sanyi-yanayi; sun fi girma a farkon bazara da ƙarshen faɗuwar ta idan

Game da

Manufar mu a Cookpad ita ce Ayi dahuwa a kullun cikin farin ciki!. Domin mun yi imanin cewa dafa abinci shine mabuɗin samun farin ciki da rayuwa mafi koshin lafiya ga mutane, al’ummomi da kuma duniya. Muna ba da ikon dafa abinci a duk faɗin duniya don Taimakon juna ta hanyar raba girke-girke da shawarwarin dafa abinci.

Post a Comment

0 Comments