Amfani da tasirin da Ayaba keyi ga lafiyar dan Adam a bangaren saduwa da iyali

Amfani da tasirin da Ayaba keyi ga lafiyar dan Adam a bangaren saduwa da iyali


 Akwai nau’ikan abinci da dama dake kara lafiya da kuzari a jikin mutane. Ayaba na daga cikin ‘ya’yan itace dake taimakawa halittun jikin mutum, musamman wajen tasirinta ga kuzarin ‘ya’ya maza.

Bincike ya tabbatar da cewar cin ayaba guda daya a kowacce zai matukar inganta lafiyar ‘ya’ya maza ta hanyoyi da dama.

Bayan kasancewar ta abinci maras maiko, ayaba na taimakon aiyukan halittun jikin mutum da su ka hada da; cire kitse maras amfani daga jikin mutum, tana inganta aikin kwakwalwa ta hanyar kara ma ta karfi, sannan tana saka jiki samar da sindarin “serotonin” da ke saka walwala da annashuwa.

A cikin ayaba akwai sinadarai da dama da suka hada da; vitamin A, B, E da PP, sinadarin kalshiyum, ayon, sodiyom, maganeziyum, da fasfaros. Wadannan sinadarai na da matukar tasiri wajen inganta aikin kwakwalwa da halittun jima’i.

Sai dai masana sun ce akwai wasu yanayi da idan mutum ya samu kansa a ciki, to ya kauracewa cin ayaba, yanayin su ne; idan jinin mutum na samun matsalar yawan daskarewa, idan mutum na da matsalar toshewar jijiyoyin jini a cikin zuciya, da ma su fama da cutar da sukari.

Amfanin ayaba bai kare iya nan ba, binciken masana ya tabbatar da cewar yawan cin ayaba na hana jini ya hau sannan tana maganin matsalolin uwar hanji.

Manyan Masana lafiyar gaba sun gano cewa itama ayaba tana kunshe da sinadarin kamar irinsu potassium, hakan ya sa masanan suka bayyana yadda ta ke karawa namiji kuzari, musamman idan ya ci mintuna kadan kamar minti 35haka kafin saduwa da iyali.

Post a Comment

0 Comments