Babban bankin Najeriya CBN ya umarci dukkan bankunan kauwanci na kasar da su fara biyan masu ajiya a bankunan sababbin takardun naira daga cikin bankunan ba kamar yadda ya umarce su da su rika biyansu ta na’urar cirar kudi ta ATM ba.
Wannan umarnin na zuwa ne bayan da harkokin kasuwanci suka kusan tsayawa cak bayan da gwamnatin Najeriya ta fitar da sababbin takrdun kudin na naira 200 da 500 da 1,000.
Cikin wata sanarwa da daraktan sadarwa na bankin Osita Nwanisobi ya sanya wa hannu, CBN ya lura da wasu miyagun halaye da ‘yan kasar ke nunawa na sayarwa da yin jifa da sababbin takardun kudin a iska da tattaka su yayin wasu bukukuwa.
Nwanisobi ya ce babban bankin ya hada gwiwa da rundunar ‘yan sandan Najeriya da hukumar tara haraji ta kasa da ta EFCC domin hukunta wadanda aka kama suna taka dokokin kasar, musamman wadanda suka jibanci yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.
Bankin ya kuma gargadi ‘yan Najeriya da su guji halayyar wulakanta takardun kudin kasar musamman a yayin da suke bikin zagayowar ranar haihuwa da na aure da na binne mamata.
0 Comments