Dan Uwa Ga Hadin Magani Ga Wanda Bata Dadewa Yana Jima’i Da Na Karfin Azzakari

Dan Uwa Ga Hadin Magani Ga Wanda Bata Dadewa Yana Jima’i Da Na Karfin Azzakari


 Da farko yan uwa ina so kuyi duba zuwa wadan nan bayanai da zanyi muku domin sunfi maganin Muhimmanci,kuma yana da kyau indai kana da matsalar da aka lissafa a sama kasan wadan abubuwan.

Matsalar mazan yanzu aksari wasu ba cuta ce dasu ba matsala ce wacce ta shafi zamantakewar aure,wasu kuma matsaloli na rayuwa na yau da kullum,amma idan baka san wannan ba kowannne Lokaci kaji ana bayani matsala irin taka sai ace sanyi ace basir ace hawan jini ace iska ce.

Amma idan ka karbi maganin kasha ba wani bayani kamar kasha ruwa,kasha maganin amma matsalar ka tana nan,kuma mutum bazai zauna yayi nazari ya gano meke damun sa ba,domin munfi damuwa musha magani matsala,ba tare da munsan abinda ya jawo ta ba.

Daga cikin Abubuwan da suke jawo saurin kawowa ko daukewar shaawa akwai wadan nan matsaloli:

1. Gajiya.

2. Damuwa.

3. Rashin bacci isasshe.

4. Matsalar zaman Aure tsakanin mata da miji.

5. Rashin samun abinci masu gina jiki.

6. Rashin motsa jiki.

Wadan nan a takaice na kawo muku su,idan kuka duba zaku ga duk cikin wadan nan abubuwa babu mata lalura ko cuta a ciki,amma suna daga cikin manyan dalilai da suke jawo rashin shaawa rashin jin dadi da saurin kawowa a lokacin saduwa.

Kana bukatar bacci mai kyau domin kwakwalwar ka ta samu hutu da nustuwa,kana Búƙatar abinci masu gina jiki domin samun sinadarai da jikin ka yake bukata,kana bukatar daidaito tsakanin ka da iyali domin a duk lokacin da kake bukatar ta ka zama kana da kwanciyar hankali.

Daya daga cikin Abubuwan nan idan ya tafi ba daidai ba,tofa ba yadda zaai a samu jima’i mai amfani,kodai ayi shi babu jin dadi ko ayi ba jima’i ayi Inzali ko ayi amma maniy yaki yazo,ko azo zaai jima’i gaban yaki ya tashi duka irin Matsalolin da ake samu kenan.

Saboda haka yan uwa ina bamu Shawara mu rika kiyayewa wadan nan abubuwa sai ka jika kowanne lokaci da karfin ka da kujarin ka a lokacin aiki da kuma jima’i.

Sannan insha Allah bayani na gaba zan kawo abubuwa da zaa hada idan an samu matsala irin wannan domin a samu waraka a rabu da matsalar baki daya.

Allah Ya A Dace Ameen

Post a Comment

0 Comments