Idan kina fama da sanyi wanda farin ruwa ke fita daga farjin ki karanta wannan rubutun domin samun mafita

Idan kina fama da sanyi wanda farin ruwa ke fita daga farjin ki karanta wannan rubutun domin samun mafita


 Kunya tana daya daga cikin abubuwan da suke hana wasu mutanen musamman mata, bayyana damuwar su ta bangaren kula da lafiya, wanda hakan za’a iya kallon sa da kuma fassara shi ta fuskoki guda biyu.

Fuska ta farko dai ita ce, a duk inda mace take an santa da kunya, don haka ba kowa zata iya tunkara ba ta fada masa abinda yake damunta na bangaren daya shafi al’aurar ta.

Fuska ta biyu kuma, da yawa daga cikin jinsin mata suna nuna gazawa wajen neman ilimi akan yadda zasu gyara wasu sassa da kuma bangarorin jikin su dake bukatar a gyara su.

Yana dakyau mace ta kasance cikin tsafta, domin kanta da kuma cikar addinin ta, wannan tasa duk abinda ya kamata ace za kiyi kafin aure, a tabbatar an koya tun daga gida.

Kasantuwar sanyi yana da illa sosai musamman a jiki da kuma lafiyar mata, hakan yana da matuƙar tasiri ta hanyoyi da dama, da kuma mabanbanta. Hakan tasa muka ga ya dace mu wayar wa mutane dakai game da hanyar da zasu bi wajen magance matsalar su.

Mata da yawa suna ƙorafi akan, ko kuma sakamakon fitar ruwa ta gaban su, wanda wasu lokutan yana zuwa da wari sosai, duk da yake babu zafi lokacin da yake fita. Amma kuma alama ce daga cikin alamun sanyin mara, wanda akasari ya fiya bayyana a garesu.

To, ga duk macen da take son magance wannan damuwa, sai ta nemo abubuwa kamar haka.

Tafarnuwa
Garin kistul hindi
Saiwar zogale
Saiwar kanunfari

Yadda ake wannan haÉ—in shine kamar haka:

A lokacin da kika samu wadannan ingantattun kayan hadin, sai ki karkato da hankalin ki wajen fahimtar yadda zaki hada su domin magance damuwar ki ko kuma nace matsalar ki, wadda ita ce ciwon sanyi mai fitar da farin ruwa daga farjin ki.

Don haka zaki samu tafarnuwa mai kyau ki jajjaga ta, sai ki hadashi da sauran kayan hadin ki tafasa a cikin tukunya ko kwano mai kyau da tsafta. Bayan ya gama tafasa sai ki tace ruwan yadda babu cito na kayan da kika tafasa. Daga nan kuma sai ki rika sha har tsawon lokacin da zai kare.

Post a Comment

0 Comments