Masana sun ce miyar kuka na ƙara wa mata ni’ima da ƙarfin mazakuta ga maza

Masana sun ce miyar kuka na ƙara wa mata ni’ima da ƙarfin mazakuta ga maza


 Kuka tana kunshe da muhimman sinadarai masu gina jiki kuma masu inganta lafiya

Kuka bishiya ce mai asali da ake samu a nahiyar Afirka da kuma wani yanki na kasashen Larabawa.

A al’adance bishiyar kuka tana da matsayi da muhimmanci ga abinci da magungunan mutanen Afirka.

Kuka tana kunshe da muhimman sinadarai masu gina jiki kuma masu inganta lafiya, kamar yadda  ta bayyana a wani bincikenta game da amfanin kuka ga lafiyar dan Adam.

Tun daga daga ganyen kuka da ɓawon da ƴaƴan kuka dukkaninsu suna da sinadarai masu amfani sosai a jikin mutum.

Mujallar ta ce kuka tana ƙunshe da kusan dukkanin sinadaran da jikin mutum yake buƙata – Kuka na da sinadarin Calcium da ke taimakawa wajen ƙwarin kashi da hakori da sinadarin magnesium wanda yake daidaita jini.

Kuka tana kuma da sinadarin iron wanda yake kare jiki daga kamuwa da cutar rashin jini, haka kuma kuka tana da sinadarin potasium da ke sasaita jini.

Sannan uwa uba sinadarin Vitamin C ya fi yawa a kuka wanda ke yaƙi da cututtuka.

Sauran sinadaran da ke cikin kuka sun haɗa da sinadarin cabonhydate da protien da vitamin D da kuma sinadarin fibre da ke sa abinci saurin narke wa a jiki.

Babban sinadarin da ke cikin kuka

Bincike ya nuna kuka tana samar da kusan rabin sinadarin Vitamin C da jikin mutum da ya haura shekara 18 ke buƙata.

Maijidda Badamasi Shu’aibu Birci malama kuma ƙwararriya kan abinci mai gina jiki ta ce wani binciken masana ya gano cewa kuka ta fi lemun zaƙi sinadarin vitamin C da linki 10, haka ma lemun tsami.

ta ce kuka tana dauke da kashi 58 na Vitamin C da mutum yake buƙata a rana.

Malama Maijidda ta ce zaren kuka ya fi yawan sinadarin Vitamin C, inda ta ce ana amfani da shi ga masu kansa.

“Mun taba amfani da zaren kuka ga mai cutar kansa,” in ji ta.

Amfanin Vitamin C ga jikin ɗan Adam ya haɗa da:

Vitamin C sindari ne da ke kare ƙwayoyin halitta da kiyaye su cikin ƙoshin lafiya.

Yana ƙara lafiyar fata da hanyoyin jini da lafiyar ƙashi da kuma ɓargo

Vitamin C na taimakawa wajen saurin warkewar ciwo.

Masana sun ce ga ƙa’ida ƴan shekara tsakanin 19 zuwa 64 suna buƙatar 40mg na vitamin C a rana.

Kuma an fi samun sinadarin vitamin C a abincin da mutane suke ci kuma ana buƙatar sinadarin a kullum.

Miyar kuka ta fi alayyahu da kuɓewa amfani a jiki

Tun daga daga ganyen kuka da ɓawon da ƴaƴan kuka dukkaninsu suna da sinadarai masu amfani sosai a jikin mutum

Miyar Kuka – ta fi dukkanin sauran gayyakin da Hausawa ke miya da su amfani ga jiki saboda yawan sinataran da ta ke dauke da su, a cewar masana.

Malama Maijidda ƙwararriya kan abinci mai gina jiki ta ce kuka ta fi alayyahu da kuɓewa cikin ire-iren gayayyaki da ƴaƴan ita ce da Hausawa ke yin miya da su a abinci.

Malamar ta ce yadda mutanen ƙauye ke yawan shan kuka yana ƙara masu lafiya, “shi ya sa yawancin cutukan da ake yi a gari da wuya a same su ƙauye.”

Ta ce kuka tana warkar da cututtuka da dama, kuma mutane ba su san amfanin kuka ba ne ya sa suke gujewa amfani da garinta ko ganyenta musamman a abinci.

Maganin da kuka ta ke yi

Kuka tana maganin zazzabin maleriya

kuka tana maganin tarin fuka TB

Tana kara ingana garkuwar jiki

Kuka tana ƙara jini a jiki

Kuka tana maganin gudawa

Kuka tana maganin hakori

Kuka tana maganin ulsa

Kuka tana rage ƙiba

Baya ga waɗannan, malama Maijidda ta ce idan ana shan kuka ba zai sa mutum ya samu kumburin ciki ba saboda rashin narkewar abinci sakamakon sinadarin fibre da ke cikinta.

Haka kuma ga wadanda ke son rage tumbi ana iya shan ganyen kuka domin yana narkar da kitse.

Masaniyar ta ce kuka tana maganin ciwon ulsa – “ga mai ulsa zai kaɗa ganyen kuka a ruwa a sha, cikin lokaci kaɗan zai samu saukin ulsa.”

Kuka tana ƙara ni’ima ga mata da mazakuta ga maza

Masana sun saboda tasirin kuka wajen inganta ruwan jikin mutum, tana kuma tasiri wajen ƙara ni’ima ga mata.

Yadda ya kamata mata su yi amfani da kuma a cewar malama Maijidda, za a samu sassaƙin kuka a wanke sosai sai dinga sha kofi ɗaya da safe da yamma.

Sannan ta ce kuka tana kara wa maza karfin jiki da mazakuta. Haka kuma mazan da ke son jikinsu ya buɗe kuka tana taimakawa saboda sinadaran da ke cikinta.

Yadda ya kamata a yi amfani da kuka

Ana busar da ganyen kuka a niƙe a tankaɗe a yi miya domin cin tuwon dawa ko masara ko shinkafa ko alkama

Kamar yadda aka yi bayani tun a farko cewa kuka tana da matsayi musamman a abincin Hausawa.

Hausawa suna yin miya da ganyen kuka. Ana busar da ganyen kuka a niƙe a tankaɗe a yi miya domin cin tuwon dawa ko masara ko shinkafa ko alkama. Haka kuma Hausawa sukan yi amfani da kuka wajen yin Ɗanwake

Amma masana sun ce ɗanyen kuka ya fi amfani fiye da busashen garin kuka da ake miya da shi.

Malama Maijidda ta ce yadda ake busar da kuka yana kashe wasu sinadaran da ke ƙunshe a cikinta – saboda rana da aka shanya kukar tana kone sinadarai da dama.

Ta ce ɗanyen ganyen kuka ya fi amfani fiye da busashen garin kuka ƙarin lafiya da sinadarai a cikin miya.

Sannan ba a son idan za a yi miyan kuka a bari ta sha wuta sosai domin yawan dafuwa zai rage yawan sinadaran da ke cikin kuka, a cewar malama Maijidda.

Shin ko kuka na da wata illa?

Post a Comment

0 Comments