Sha Yanzu Magani Yanzu: Idan Kana Son Ka Jima Kana Saduwa Da Matarka To Ga Albishir

Sha Yanzu Magani Yanzu: Idan Kana Son Ka Jima Kana Saduwa Da Matarka To Ga Albishir


 Idan dai matsala ce wadda ta shafi bangaren rayuwar magidanta, musamman rashin samun haihuwa ga mace, ko kuma rashin karfin mazakuta ga namiji, to wannan hadin maganin yana da matukar fa’ida da amfani sosai.

Amma banda wannan maganin, idan kana da matsalar karancin sperm (maniyyi) ko karyewar maniyyi to kada kayi amfani dashi.

Sannan daina amfani da shi kuma zai É—auki kwanaki 3. Amma insha Allah daga ranar da ka fara amfani da shi za ka ga canji a yanayin jiki wajen aiwatar da ayyuka na yau da kullum.

Domin yin wannan hadi, akwai abubuwan da za’a nema domin hada maganin ya zama cikekke dari bisa dari (100%), wadannan sun hada da:

Madara ta ruwa

Garin Kimba (Negro pepper).

Bayan kun samo wadannan abubuwan naku ga yadda zaku hada su:

Da farko za’a samu madara rabin gwangwani da ruwa a zuba a cikin kofi, sai a zuba garin Kimba rabin cokali, bayan wani dan lokaci kadan sai a juya sosai, bayan ya kai kimanin minti 30 da shan wannan hadi, sai kuma a tunkari iyali domin biya musu bukata.

Amfanin shan Kanunfari da madara.

Da yawa mutane suna neman magani ne,amma sai su tsallake asalin magani su tafi neman wani abu daba bisa rashin sani.

A yau insha Allahu zan sanar daku 2 daga cikin amfanin shan Garin kaninfari da madara ta ruwa ko nono.

(1) Yana magance matsalar saurin kawowa.

Matsalar saurin kawowa matsala ce da take damun mafi yawan magidan ta a wannan lokaci musamman ma wadan da basu da manyan shekaru, wanda hakan a tare dasu babbar illa ce da kuma barazana a zamantakewar su da abokan zaman su.

(2) Matsalar infection.

Infection wanda aka fi kira da sanyin mara, shima yana daga cikin ciwokan dake damun jama’a mata da maza yan mata da zawarawa kai harda matasa.

Shin ta wacce hanya zaa iya magance wadannan matsaloli da kaninfarin.

(1) Garin kaninfari.

(2) Madara ta ruwa/nono.

Za’a samu garin kaninfari rabin karamin chokali a zuba a ciki karamin kofi na madara ta ruwa ko nono a juya sosai sannan a sha,ana sha ne sau daya a rana na tsawon kwana 3 kacal.

Post a Comment

0 Comments