Yadda Mace zata gane tana da budadden gaba da kuma yadda zata tsuke gaban nata koda ya bube

Yadda Mace zata gane tana da budadden gaba da kuma yadda zata tsuke gaban nata koda ya bube


 1. Mafi yawan mata masu fama da matsalar buÉ—aÉ—É—en gaba na fama da matsalar rashin riÆ™e fitsari , wato É—igar fitsari.  Digar fitsarin zata iya faruwa a lokacinda kika É—auki wani abu mai nauyi, ko lokacinda kika yi dariya, tari, ko atishawa. Wannan alamace cewa mace nada budadden gaba.Yawan shekaru, yawan haihuwa , yawan jima’i, tiyatar likita (Æ™arin kofa) ko wani rauni a  gaban mace, ko   tsayawar al’ada (menopause) saboda karancin sinadarin “estrogen” na iya sanya raunin tsokokin farji wanda daga Æ™arshe zai iya haddasa buÉ—ewar tsokokin bangon  farji masu matse zakari.

2. Hanya ta biyu da zaki iya sanin ko kina da gaba mai faÉ—i itace: ki saka É—an yatsanki guda (manuni) cikin gabanki sa’annan kiyi Æ™oÆ™arin matse dan yatsan da tsokokin farjinki.  Idan har ki gwada yin hakan kuma ya zamanto baki iya jin kina matse dan yatsan da farji to zaya iya zama kina da babban wuri. Bugu da Æ™ari, idan kika saka yatsa 2 ko 3, misali manuninki da kuma yatsan tsakiyar hannnunki (mafi tsawo) , kuma baki ji wata alamar bangon farjinki yana matse yatsun ba to yiwuwar itace kina da buddden farji.

3. Idan ya zamanto yana da wuya kamin kiji ƙololuwar dadi (orgasm)/kawowa lokacin saduwa. Yana iya yiwuwa alamar budadden gaba ne. Haka kuma, raguwar jin dadi ba kamar daba shima na iya zama alamar.

4. Idan ya zamanto mace tana wasa da gabanta domin biyan buÆ™atarta kuma tafi sha’awar ta saka wani babban abu a gabanta akan Æ™arami – wato bata jin dadin Æ™aramin abu idan ta saka a farji sai babba. Shima alamace cewa mace nada girman farji.  A baya munyi bayani da tsoratarwa akan wasa da gaba. Yana da illa ga lafiya da rayuwar auren ‘ya mace. Don haka sai a kiyaye.

5. Idan ya zamanto kina shan wahala kamin ki gamsar da mai gidanki wajen jima’i ba kamar daba.

6. Idan ya zamanto sai kin matse ko haÉ—e cinyoyin ki biyu  sosai sa’annan kike jin dadin jima’i da maigidanki. Wannan ma yana iya zama alamar budadden gaba. Duk da dai cewa wani lokacin yana iya zamantowa mijin ne keda Æ™aramar al’aura. Amma idan kamin haihuwarki babu wannan matsalar sai daga baya to sai ki zargi budewar gaba.

7. Idan ya zamanto kina jin Æ™arar fitar iska daga farjinki lokacin da maigidanki yake saduwa dake , iskan kamar fitar “tusa” amma ba tusa bace (fanny farting) kuma babu wari. Iskan yana shiga yana fitowa  lokacinda maigida yake kaikawo. Wannan alamace kina da budadden farji.

MINENE HANYOYIN TSUKE FARJI ?

Akwai hanyoyi da dama na matse gaba musamman bayan haihuwa wanda sun hada da hanyoyin magani, motsa jiki (exercise), tiyatar likita domin rage girman farji da sauransu. Wasu hanyoyin nada illa ga lafiya , wasu kuma hanyoyin basa da wata matsala ko hadari kamar dai yanda likitoci ke bayani. Wasu daga cikin hanyoyin:

1. Motsa jiki , hanyoyin motsa jiki na zamani domin matse gaban mace suna da yawa (such as kegel exercises) da sunaye. Motsa jikin ya shafi horo da mace zata iya bawa jikinta domin ya zamanto tsokokin gabanta masu motsi sun kara ƙarfi da tsukewa.

Misali, wata kwararriyar likita a India Dr. Sangeeta Gomes ( Consultant Obstetrician and Gynaecologist) , ta nuna cewa mace zata iya inganta tsukewar gabanta idan tana yin motsa jikin dauke numfashi (breathing exercises).

Zaki dauke numfashinki na tsawon ‘yan daÆ™iÆ™oÆ™i (seconds) kadan sannan ki tsuke (tsokokin) farjinki matakam na tsawon wani lokaci a lokacinda kike mai dauke numfashin.

Za kiyi hakan a kowace rana, sau 10 ko 15. Zaki iya yin hakan a kicin lokacinda kike aiki, a ofis, a tsaye ko a zaune , a ko ina  kuma  a ko wane wuri bata tare da ma wani yasan abinda kike yi ba.

Sa’annan  zaki yawaita cin ƳaÆ´an itatatuwa (kayan marmari) da abincin ganye (vegetables). Wannan ko shakka babu zai taimakawa  mace wajen matse gaba domin gyara aurenta. Wani nau’in motsa jikin kuma shine ake cema “Kegel exercise”.

Toh  yaya ake yinshi? Dr. Gomes ta nuna cewa idan kina yin fitsari sai ki tsaida fitar fitsarin, wato ki  riÆ™e fitarin, ki danne sa na tsawon daÆ™iÆ™oÆ™i 10 , wato ki Æ™irga 1 zuwa 10 sa’annan ki saki fitsarin a hankali a hankali. Zaki iya yin hakan sau 2 ko 3 a rana idan za kiyi fitsari. Shima wannan nau’in motsa jikin na tsuke gaban mace.

2. Hanya ta biyu shine wanke gaba da ruwan sanyi mai Æ™ankara. Yana  taimakawa  wajen matse gaba amma sai an hada da motsa jikin da muka yi bayani. Wannan yana daga cikin hanyoyin da Dr. Gomes ta zayyana.

Amma zaifi dacewa ace sai mace ta gama wankan jegonta na kwana 40 kwatakwata sa’annan tayi amfani da ruwan sanyin , wato bayan ta koma “normal”. SaÉ“anin yanda al’adar Bahaushe tayi imani dashi cewa ruwan sanyi na lalata gaban mace ,wasu likitocin a wasu al’adun na ganin yana matse gaba.

3. Yin amfani da aluf (alum). Aluf yana matse gaba sosai sai dai likitoci na tsoratarwa akan yin hakan saboda da sinadarin kemikal ne.

4. Yin tiyatar likita domin rage budewar farji. Wannan ma hanya ce ta zamani amma ana tsoratarwa akan yin hakan saboda wasu dalilan lafiya.

5. YunÆ™urin tsuke gaba a lokacin saduwa, wato ki matse farjinki ta ciki lokacinda mijinki yake kaikawo. Zaki yawaita yunÆ™uri domin tsuke gabanki domin mijinki yaji alamun ana riÆ™e masa al’aura tamkar zobe zagayen gabansa. Idan mace na yawaita yin da haka to zai zama É—abi’arta kuma nan gaba ba zata san ma tanayin hakan ba saboda ta riga ta horar da jikinta, kuma hakan zai inganta jin daÉ—in mijinta sosai. Allah Ya taimaka.

6. Da sauransu.
Za’a iya neman taimako na musamman daga cibiyar mu domin magance wannan matsala wacce za’a haÉ—a da bayanan da mukayi anan domin samun sakamako mai kyau, da yardar Allah.

Post a Comment

0 Comments