Yadda za’a hada ingantaccen maganin karfin maza ga wadanda suke da lalura ta raunin mazakuta

Yadda za’a hada ingantaccen maganin karfin maza ga wadanda suke da lalura ta raunin mazakuta


 Raunin azzakari yana daga cikin abubuwan da suke damun maza da yawa a lokacin da suke son biyawa kansu tare da iyalin su bukata wajen yin jima’i. To babban abinda ya kamata mutum yayi shine ya kokartawa kansa don binciko mafita ta waraka ga kansa da kuma jindadin mai dakin sa.

Ingantaccen karfin Maza ma’ana mazakuta yana da matukar muhummanci ga rayuwar maza musamman bangaren zamantakewar iyali, domin sautari maza kan samu matsala wajen biyawa iyalansu bukata saboda irin wadannan matsalar da suke fama da ita, wadda a karshema wata macen saki zata nema kai tsaye daga wajen abokin rayuwarta saboda wannan damuwar.

Insha Allahu wannan magani da zamu bayar a kasa ba iya karin karfin mazakutar yake ba, haka zai karawa mazakutarka Girma, Karfi wajen Jure Jima’i mai tsawo, da kuma magance matsalar sanyi ko wanne iri ne insha Allahu.

Abubuwan Da Yakamata A Nema Domin Hada Wannan Maganin Sune :

Tafarnuwa

Citta

Kununfari

Zuma

Albasa

Ga Yadda Zaku Hada Maganin Cikin Sauki ;

Za’a samu albasa mai kyau sai a nikata sosai tazama ruwa. Sannan a kawo tafarnuwa sai a nikata, amma ruwan nikan tafarnuwar yazama dan kadan.

Cittakar kuwa da Kanunfari ana dakasu sosai suyi laushi.

Bayan ka gama da wadannan abubuwa saika samo kofi da cokali saika debi kamar cokali biyu na Albasa, cokali biyu na Tafarnuwa, cokali biyu na Kanunfari da kuma cokali biyu na Citta, akarshe saika debi cokali kamar Hudu na Zuma saika hadasu gaba daya a kofin nan saika juya sosai kashanye duka.
Wannan hadi a rana sau biyu kawai za’ayi, kuma insha Allahu za’a samu kyakyawan sakamako.

Post a Comment

0 Comments