Agbu Kefas ya lashe zaben gwamna a karkashin tutar jamiyyar PDP a Jahar Taraba
Agbu Kefas, dan takarar Jam’iyyar PDP ya lashe zaben Gwamnan Taraba, kamar yadda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar.
Baturen zaben gwamnan Taraba na INEC, Farfesa Mohammad Abdulazeez, ya bayyana cewa Agbu Kefas na ya yi nasara ne bayan shi da Jam’iyyar PDP sun samu kuri’u 257,926..
Sai kuma dan takaran gwamna a karkashin tutar Jam’iyyar NNPP, Farfesa Sani Muhammed Yahaya, wanda yazo na biyu da kuriu 202,277.
Sai kuma Sanata Emmanuel Bwacha na Jam’iyyar APC wanda ya sami kuriu 142,562.
Shi dan takaran gwamna a karkashin tutar jam’iyyar PDP ya lashe zabe a kananan hukumomi goma sha daga cikin kananan hukumomi goma sha takwas na Jahar ta Taraba.
0 Comments