Kotu ta hana gwamnatin Gombe da ƴansanda kama wani ɗan jarida
Wata babbar kotun jihar Gombe ta hana gwamnatin jihar da ƴansanda kama Dahiru Kera, mawallafin wata jarida ta yanar gizo mai suna Daylight Reporters.
Tun da fari dai gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya ne ya ayyana mawallafin a matsayin wanda ya ke nema ruwa a jallo a wani yunkuri na rufe bakin ƴan jarida da ƴan adawa a jihar.
Daga bisani sai Kera ya buya, bayan da ya samu barazana daga gwamnan, wanda ya sha alwashin sai ya yi maganin sa.
A hukuncin da ya yanke kan karar mai lamba: GM/145M/2022, alkalin kotun, H. H. Kereng, ya dakatar da gwamnatin jihar da ‘yan sanda daga yunkurin kama Mista Kera.
Kotun ta bayyana cewa gayyatar da aka yi masa da kuma barazanar kama mawallafin tauye hakkinsa ne; “Musamman tanade-tanaden sashe na 34, 35, 39 da 41 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da Yarjejeniya Ta Afirka kan ‘Yancin Bil Adama da Al’umma da kuma Yarjejeniyar ‘Yancin Dan Adam ta Duniya.
Hukuncin ya ci gaba da cewa, “ci gaba da gayyata da kuma barazana ga jami’ai/wakilan wanda ake kara na daya ke yi na iya tauye ƴancin mai karar ne kamar yadda kundin tsarin mulki na 1999 ya tanada (kamar yadda aka gyara).
0 Comments