Ƙungiyar Mata da Matasa na PDP, a yau Alhamis, ta yi dirar mikiya a kan titunan birnin Kaduna, inda su ka yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da sakamakon zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha da aka kammala a jihar.
Mambobin kungiyar da suka mamaye tituna, sun kunshi mata da yawa sanye da bakaken kaya, dauke da alluna masu rubutu iri-iri.
Wasu daga cikin rubuce-rubucen sun hada da: ‘A bamu mulkin mu’, ‘Ba mu yadda da canja sakamakon zaɓe ba’, ‘Ba za mu yarda a kwace mana nasarar mu ba, da sauransu.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Sanata Uba Sani na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben kujerar gwamna da INEC ta sanar a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha da aka gudanar a ranar 18 ga watan Fabrairu.
Da ta ke zantawa da manema labarai yayin gudanar da zanga-zangar ta lumana, shugabar kungiyar, Aishatu Madina ta bayyana cewa zaben gwamnan na tattare da maguɗi.
Ta ce zanga-zangar ta biyo bayan matakin da shugabannin PDP na Kaduna suka dauka na kalubalantar nasarar APC a kotu.
Madina ta yi zargin cewa APC ta yi magudi a sakamakon zaben.
“Muna da kananan hukumomi 23 a Kaduna, PDP ta ci kujerun ‘yan majalisa 20, majalisar wakilai, Sanatoci uku da wakilai 10, ta yaya APC ta ci zaben kujerar Gwamna,” in da ta nuna mamaki kan hakan.
0 Comments