ME YAKE KAWO CIWON TSAKIYAR KUNNE

ME YAKE KAWO CIWON TSAKIYAR KUNNE


                             ME YAKE KAWO CIWON TSAKIYAR KUNNE  

Ita kunne kanta an kasa shi bari uku (3) :

1- Outer ear = wajen kunne .
2- Middle ear – Tsakiyar kunne
3- Inna ear – Cikin kunne .

Mafi yawan ciwon kunne da mutane suke complaining ciwon tsakiyar kunne ne ( Otitis media ) .

ME YAKE KAWO CIWON TSAKIYAR KUNNE :

Yana daga cikin abubuwanda suke kawo ciwon tsakiyar kunne :
1- kwayar cututtuka kamar su :
a- bakteria
b- virus
Amma mafi yawa bakteriya ne , wadannan kwayoyin cututtukan yawanci suna samun hanyar shiga ne ta makogoro zuwa tsakiyar kunne. ( akoi hanyar da tahadasu dama).

2- Anasamun ciwon kunne ta dalilin shigan wani Abu kamar Burbushin Kura , Gashin magye da sauransu ( Allergies).

HALAMUN CIWON TSAKIYAR KUNNE :

1- Mutun zaiji kamar wani abu ya cika masa kunne .
2- Rashin ji sosai
3- Zubar da ruwa a kunne
4- Jin zafi a cikin kunne .
5- kaikayin
6- Zazzabi da ciwon kai .

MENENE ALAKAR MURA DA CIWON KUNNE :

Gaskiya akoi alaka tsakanin mura da ciwon kunne , mafi yawan mura yana kama hanci da makogoro kuma idan Baku manta ba munce akoi hanyar da tahada tsakanin Makogoro da Hanci dakuma tsakiyar kunne .

Kamar yadda mukace kwayoyin cutar bakteriya , da virus da kuma burbushin kura su suke kawo ciwon kunne.
To wadannan kwayoyin cutar su suke kawo Mura kuma suna samun hanyar shiga kunne ta wannan hanyar da tahada tsakanin makoro , hanci da kunne.

SHIN DIGAWA KUNNEN MAN ZAITUN YANA MAGANI CIWON KUNNE :

Kuskure ne digawa kunne man zaitun, bama man zaitun ba ko maganin ciwon kunne irin su gentamycin bai kamata a digawa kunne ba, in bada izinin likita ba.

Dalili shine wani lokocin ana samun fujewan dodon kunne (rupture of earwax) lokocin da ake ciwon kunne to ko wanne irin abu idan yawuce can ciki zai iya kawo matsala.

MAGANIN CIWON KUNNE :

Tabbas duk wani ciwon kunne da kwayoyin cutar bakteriya takawosu ana amfanida ANTIBIOTICS wajen treatment , hakanan wanda aka samu da dalilin Burbushin kura ana amfani da ANTIHISTAMINES.

GARGADI

Diyawa daga cikin mutane idan kunnensu yana ciwo kawai zuwa suke chemist a wanke musu kunne.

Bincike ya nuna akoi sinadarai guda goma a tsakiyar kunne wanda aikinsu shine hana wasu kwayoyin cuta na bakteriya da makamantansu girma da shiga cikin kunne, a garin wanke daudan kunne idan aka wanke wadannan sinadaran to daga nan anbudewa kwayoyin cuta kofa ne .

WASSU ZA KAGA SUNA YAWAN KWAKULE KUNNE:

Amfanin “dauÉ—ar kunne” da illar Æ™waÆ™wale ta.

“DauÉ—ar kunne” wani ruwa ne mai É—an danko da dodon kunne ke samarwa domin bai wa kunne kariya, saÉ“anin yadda Bahaushe ke cewa “dauÉ—ar kunne” ce . Saboda haka “dauÉ—ar kunne” ba dauÉ—ar kazanta ba ce, face wata hanya ce da kunne ke samar wa kansa kariya daga baÆ™in abubuwa da ka iya shigowa daga waje.

Allah da ikonsa, kamar yadda kunne ne ke samar da wannan “dauÉ—ar kunne”, haka nan kunnen ke da ikon yashe wannan “dauÉ—a” da kansa.

Daga cikin amfanin “dauÉ—ar kunne” akwai:

1. Cafke dukkan nau’in Æ™ura, Æ™asa, Æ™wari ko yayi kafin su kai ga cikin kunne.

2. Kashe kwayoyin bakteriya, da sauransu.

Saboda haka kada ka yi amfani da waɗannan abubuwa don ƙwaƙwale dauɗar kunne:

1. Magogin kunne wato ‘cotton bud’ a turance.

2. Tsinken tsintsiya

3. Mirfin biro

4. Kan ashana

5. Gashin kaza, da makamantansu.

Sanya waÉ—annan abubuwa cikin kunne don Æ™waÆ™walo “dauÉ—ar kunne” na da haÉ—arin:

1. Ƙara cusa “dauÉ—ar” zuwa can cikin kunne.

2. Kareraya gasun cikin kwararon kunne, wanda suke amfani wajen kare kunne daga baƙin abubuwa daga waje.

3. Cusa irin waɗannan abubuwa na da haɗarin shigar da ƙwayoyin cuta cikin kunne.

4. Raunata gangan kunne yayin da irin waÉ—annan abubuwa suka zarme cikin kunne.

5. Shafe ko manne “dauÉ—ar kunnen” a kwararon kunne.

Haka nan, zira waÉ—annan abubuwa cikin kunne don susa ko Æ™waÆ™walo “dauÉ—ar” akai-akai zai share kwararon kunne, kuma share Æ™wararon kunnen na nufin share kariyar da Allah ya shirya wa kunne. Saboda haka, dukkan baÆ™in abubuwa na iya kutsa kai cikin kunne kai tsaye.

Kada ka É—auki É—abi’ar sa magogin kunne cikin kunne don goge “dauÉ—ar kunne” kullum.

TuntuÉ“i likitan kunne da zarar ka fara jin wani É“aÆ™on yanayi a kunnenka, ko neman shawarwari kan tsabtace kunne daga “dauÉ—ar kunnen”.

Lafiya Uwar Jiki

Post a Comment

0 Comments