Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya sake nanata burinsa na ganin ya kammala wa’adin mulkinsa domin ya koma gida ya huta.
Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron ban-kwana da jakadar Amurka a Najeriya Mary Beth a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Talata.
Wannan ba shi ne karon farko da Buhari ya bayyana burinsa na ganin ya kammala wa’adinsa ba.
“Na zaku na tafi.” Buhari ya ce kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A ranar 29 ga watan Mayu, wa’adin mulkin Shugaba Buhari zai kare.
A shekarar 2015 ya fara lashe zaben wa’adin mulkinsa na farko.
Sannan a shekarar 2019 ya sake lashe zaben da ya ba shi wa’adi na biyu wanda zai kammala a watan Mayu mai zuwa.
0 Comments