Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya taya zabbben Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf murna bisa nasarar da ya samu ta lashe zaben gwamnan jihar a zaben da aka gudanar ranar Asabar, 18 ga Maris.
Cikin wata sanarwa daga Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano, Abubakar Balarabe Kofar Naisa, Sarkin ya bayyana cewa al’ummar jihar sun karbi tsarin mulkin damokaradiyya da matuqar muhimmacin idan akayi la’akari da yadda su ka fito domin jefa kuri’unsu kamar yadda tsarin mulki ya bada dama.
Sarkin ya kuma shawarci, tare da kira ga sabon gwamnan da ya hada kai da dukkanin rukunin al’umma wajen tafiyar da gwamnati, domin yin hakan zai taimaka wajen kyautata rayuwar al’umma da kuma kawo cigaban da ake bukata domin bunkasar tattalin arziki ga jihar Kano da kasa baki daya.
Sanawar ta kuma godewa malamai da Limamai da sauran Al’umma bisa addu’ar zaman lafiya da suka dunga yi kafin da kuma bayan gudanar da zaben.
Alhaji Aminu Ado Bayero yayi fatan dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano har ma da sauran sassan kasar nan.
Ya kuma yi wa Annan addu’ar kammala mulkinsa lafiya tare da samun cigaban gwamnatinsa da habaka tattalin arzikin jihar Kano.
0 Comments