TSARIN IYALI GA MAZA (FAMILY PLANNING FOR MALES)

TSARIN IYALI GA MAZA (FAMILY PLANNING FOR MALES)


 TSARIN IYALI GA MAZA (FAMILY PLANNING FOR MALES)


Na fahimci cewa mata da yawa a cikin wannan group din suna matukar damuwa game da matsalolin da suke samu a sakamakon yin amfani da hanyoyin tsarin iyali. Matsalolin sun hada da rikicewar jinin al’ada, zubar jini daga farji babu kakkautawa, daukewar al’ada har lokaci mai tsawo, ciwon nono, ciwon kai, bacin rai, yin kiba, yin rama, raguwar sha’awar jima’i, tashin zuciya, zubar ruwa daga farji, yankewar haihuwa, da sauransu.


Domin haka, wasu mata suna yin tuhuma akan cewa menene dalilin da ya sanya masana ilimin kimiyya basu kirkiro magungunan tsarin iyali na maza ba, saidai na mata kawai? Kuma suna ganin cewa yin haka wani nau’i ne na rashin adalci a garemu, saboda hidimar iyali ta kamata ta kasance hadin gwiwa ce a tsakanin ma’aurata.


Hukumar kula da kiwon lafiya ta duniya (World Health Organization - WHO) ta bayyana ma’anar tsarin iyali da cewa shine yin amfani da magani (medication), ko na’ura (device), ko kuma yin tiyata (surgery) domin a hana mace ta dauki juna biyu, saboda ma’aurata su sami damar kula da lafiyar matar, ’ya’yanta, iliminsu, ko kuma inganta rayuwarsu to fannoni daban-daban.


YADDA MAGANIN TSARIN IYALI YAKE AIKI A CIKIN JIKI


Yawanci maganin tsarin iyali ana yinsa ne da wasu sinadarai guda biyu wadanda ake kira estrogens da progestins.

Shi estrogen yana sauya zubar sinadarin jikin mace ne domin ya hana jakar da take dauke da kwai na haihuwa (ovary) ta saki kwai (ovum) bayan mace ta gama al’ada. Wannan yana nufin idan matar bata saka kwai ba, ko mijinta ya sadu da ita, to, ’ya’yan maniyyinsa (sperm cells) ba zasu sami kwai wanda zasu kyankyashe ba balle har a sami juna biyu.


Shi kuma progestin yakan lullube kwai na haihuwa ne wanda matar ta saka ya sanya fatar kwan tayi kauri ko tsauri sosai ta yadda ’ya’yan maniyyi ba zasu iya huda fatar ba balle su kayankyashe kwan.


Idan kuma na’ura aka yi amfani da ita, kamar condom, to, maniyyin ba zai shiga farjin matar ba ma balle ya kyankyashe kwan.

Idan kuma tiyata akayi, to, ana yanke ko kuma toshe hanyar da kwan haihuwa yake biyowa ne (fallopian tube), ko kuma hanyar da ’ya’yan maniyyi suke biyowa (epididymis) su shiga cikin farji.


ABIN LURA


Yawancin sinadaran da suke cikin kwayoyin maganin tsarin iyali (birth control pills), a kwai su a cikin jikin mace wadanda Allah ya halicce ta dasu. Dan-adam ne yake tatso su ya sarrafa su ya kuma zuba su a cikin kwayoyin magani domin su sauya yanayin zubar wadancan sinadaran na asali da Allah ya halitta a jikin mace. Wannan yana nufin cewa halittar jikin mace ce kawai zata iya jure matsalolin da magungunan tsarin iyali suke haifarwa, amma ba namiji ba. Misali, magungunan suna haddasa zubar jini, kuma namiji baya da halittar da zata iya fitar da wannan jinin daga jikinsa. Suna haifar da ciwon nono, alhalin kirjin namiji ba zai iya daukar wannan larur ba. Suna haifar da ciwon mara, alhalin marar namiji bata da rsarin da zata dauki ciwon mara mai tsanani, da dai sairansu.


Idan mata suka ce lallai suna so maza dole su fara amfani da magungunan tsarin iyali, to, lallai fa sun jawo babbar magana. Kamar dai suce suna so suma maza su fara shayar da nono ne, ko kuma su fara jinin al’ada.


Wannan shine dalilin da ya sanya manyan masana ilimin kimiyya na duniya har yanzu basu iya fiyar da wata sahihiyar hanya ta tsarin iyali ta maza ba.

A halin da muke ciki yanzu, hanyoyin tsarin iyali na maza sune:


1. Amfani da hular mazakuta (condom).


2. Yin tiyata domin yake hanya da ’ya’yan maniyyi suke biyowa domin su shiga farjin mace (surgical vasectomy). Idan aka yi wannan tiyatar, to, shikenan namiji ba zai kara haihuwa ba har abada.


3. Fitar da azzakari daga farji a lokacin da namiji zai yi inzali (withdrawal method). Wannan hanyar bata cika amsuwa ba wajen ma’aurata, domin tana haifar da rashin gamsuwa.


4. Yin allura a marainan namiji (reversible inhibition of sperm under guidance- RISUG). Yanzu an dauki shekaru da dama ana kokarin tabbatar da wannan hanyar. Amma matsalar ta ita ce tana da tsada, kuma akwai hadarin cewa ’ya’yan maniyyin namiji zasu iya mutuwa kwata-kwata


Post a Comment

0 Comments