ALAMOMI MASU HATSARI LOKACIN GOYON CIKI WATO LOKACIN JUNA BIYU WANDA YAKAMATA KOWACCE MACE TAKIYAYESU DON RABUWA DA CIKIN LAFIYA

ALAMOMI MASU HATSARI LOKACIN GOYON CIKI WATO LOKACIN JUNA BIYU WANDA YAKAMATA KOWACCE MACE TAKIYAYESU DON RABUWA DA CIKIN LAFIYA


  ALAMOMI MASU HATSARI LOKACIN GOYON CIKI WATO LOKACIN JUNA BIYU WANDA YAKAMATA KOWACCE MACE TAKIYAYESU DON RABUWA DA CIKIN LAFIYA


 1- Zuban jini daga mara.

 2- Cizon harshe da yawan mika.

 3- Ciwon kai da rashin gani ko gani dishi dishi.

 4- Zazzabi da ciwon jiki.

 5- Ciwon ciki

 6- Karanci ko yawan numfashi.

 7-Yawan ciwo.

 8- Kumburin kafa, yatsu, da kuma fuska.


Idan mace taga alamomin tsorota (alamomi masu hatsari ( to tayi gaggawar zuwa asibiti koda lokocin awun ta baiyi ba.


Wadan su abubuwa da mai juna biyu za ta kiyaye


1- Ya kamata mai juna biyu ta guji aikata duk wani abu da zai rika sanya mata gajiya. Ana so mai juna biyu ta rika aikata aikin da ba zai bukaci karfi da yawa ba.


2- Ya kamata mai juna biyu ta rika hira da mutane domin cire mata gajiyar kwakwalwa, wanda gajiyar kwakwalwa na haifar da gajiyar jiki, yakan kuma sanya mai juna biyu ta rika jin kamar ba ta da lafiya (queasy ko nausea).


3- Ya kamata mai juna biyu ta rika hutawa, sannan ta rika motsa jiki a hankali.


4- A lokacin da ciki ya fara girma kamar daga wata biyar ko shida. Yakamata mai juna biyu ta guji:


- Kusantar sinadarai masu cutarwa.

- Daukar lokaci wajen aiki.

- Dadewa a tsaye.

- Daga abu mai nauyi.

- Zama a wajen da ake yawaita hayaniya ko surutu mai karfi.

- Zama a wurin da akwai injina masu kara.

- Zama a muhallin da ke da sanyi da yawa. Ya kamata mai juna biyu ta guji shan ruwa mai sanyi, ko yawaita zama a karkashin na’urar AC na tsawon lokaci.

- Zama a muhallin da ke da sananin zafi.

Yanada kyau duk wata mace idan tanada ciki taji Wani sauyin dabata ganeba tayi gaggawan tuntubar likita Kuma tana zuwa AWO akan lokaci, ubangiji yasauki kowacce mace me ciki lafiya Wanda Basu haihuwa ba Allah yabasu masu Albarka.

📝 (shirin kiwon lafiya) Lafiya uwar jiki.

Post a Comment

0 Comments