ABUBUWAN 8 DA YA KAMATA A LURA DASU KAFIN A DORA MACE AKAN TSARIN IYALI KO MAGUNGUNAN TAZARAR HAIHUWA WATO FAMILY PLANNING

ABUBUWAN 8 DA YA KAMATA A LURA DASU KAFIN A DORA MACE AKAN TSARIN IYALI KO MAGUNGUNAN TAZARAR HAIHUWA WATO FAMILY PLANNING


 ABUBUWAN 8 DA YA KAMATA A LURA DASU KAFIN A DORA MACE AKAN TSARIN IYALI KO MAGUNGUNAN TAZARAR HAIHUWA WATO FAMILY PLANNING


Ya kamata mata su sani cewa akwai abubuwan da ya kamata su kiyaye Kamin amfani da ko wane nau'in tsarin tazarar haihuwa wato family planning methods na zamani. 


Ya kamata ma’aikatan lafiya suyi la’akari da wadannan abubuwan domin samun saukin laulayin da magungunan tazarar haihuwa suke haddasawa:


1. Shekarun haihuwa (age) Ana bukatar sanin shrkarun wacce za a dora akan tsarin tazarar haihuwa. 


2. Nauyin jiki/kiba (body weight). Ba a yi wa mata ma su babban jiki sai bisa ga umurin likita. 


3. Hawan jini (hypertension). Hawan jini yana qara haddasa wasu cutuka a lokacin da ake amfani da wasu tsarin tazarar haihuwa. 


4. Cututtukan nono, zuciya, koda, hanta, da sauransu (cronic illnesses)


5. Cututtukan mahaifa, kamar cututtukan da ke addabar mata da aka fi sani da ciwon sanyi (uterine diseases)


6. Maccen da ke shayarwa akwai na su tsarin tazarar haihuwa na musamman duba da Jaririn da suke shayarwa (breast feeding)


7. Bijirewar jiki ga magungunan kamar robar da ake dasawa macce a hannu. A likitance ana Kiran sa (allergy).


8. Ya kamata mata ku sani cewa kasantuwar abokiyar ki ta yi amfani da tsarin tazarar haihuwa ba ya zama dalilin da zai sa ki yi amfani da irin sa sai da shawarar maaikatan lafiya. 


Tsarin tazarar haihuwa mafi kyau shine tsarin da ya dace da jikin ki.

Post a Comment

0 Comments