Kano: An kai maroƙi kotu bisa zargin sace wayoyin abokan ango a wajen daurin aure


Kano: An kai maroƙi kotu bisa zargin sace wayoyin abokan ango a wajen daurin aure


 Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta gurfanar da wani mutum mai suna Bashir Abubakar Brigade a gaban wata kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Fagge ‘Yan Alluna bisa zargin laifin satar wayoyin abokan ango a yayin daurin aure.



Daily Trust ta rawaito cewa an kama Bashir ne bisa zargin satar wayoyin hannu guda biyu da kudinsu ya kai Naira dubu 125 da kuma Naira dubu 25.

Lauyan masu shigar da kara na Jiha, Barr. Zaharaddeen Mustapha, ya karanta wa wanda ake zargin laifukan da suka hada da hada baki da kuma sata.

Sai dai ya musanta zargin da ake masa, inda ya jaddada cewa shi ba barawo ba ne, maroƙi ne kawai.

Daga bisani kotu ta bada belinsa da sharadin ya kawo dan uwansa na jini da kuma takardar shaidar wani gida da ya mallaka.

Alkalin kotun, Khadi Umar Lawan Abubakar ya dage sauraron karar har zuwa ranar 25 ga watan Nuwamba domin bayar da shaida.


Daily Nigerian Hausa

Post a Comment

0 Comments