Sirrin hana miji karin aure
Ga matar da ke son zama ita kadai a wajen mijinta, sai ta bi shawarwarin nan.
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili. Ga bayani kan hanyoyin da mace za ta bi don ta zama daya tamkar da hudu a wajen mai gidanta.
Kamar yadda Allah Ya ni’imtar da maza da umarnin auren mace sama da daya, mata ma Ya ba su wasu hikimomi da hanyoyi ga mai son ta rike mijinta kawai ta hanyar zame masa mace tamkar hudu ta yadda ba zai yi sha’awar karin aure ba, domin komai na bukatarsa za ta warkar masa da su.
Ga matar da ke son zama ita kadai a wajen mijinta, sai ta bi shawarwarin nan masu zuwa:
Da farko ya danganta da halayyar mijinki, ta fuskar sha’awarsa da shau’ukan zucinsa. In mijinki mai bukatar mata hudu ne wajen ibadar aure, to dole mace ta kasance akalla tana da karfi da kuma zuma ko dandanon mace uku, wanda ba karamin aiki ba ne, sai macen da ta amsa sunanta ko in ce giwar mata.
Sannan in mijinki mai yin aure ne don ya yi alfahari da matansa ko ya biya wata bukata ta sha’uka da danshin zuciyarsa, dole ne mace ta kasance mai canja halayyarta a-kaia-kai.
Sannan ba sai na fada ba, ladabi da biyayya da kwalliya da tsabta da tarairaya da wasanni na soyayya, shagwaba da sauran kananan abubuwa masu muhimmanci ne wajen hana miji karin aure.
Haka kuma mu lura, da yawa daga maza suna karin ne in zumar matansu na farko ta fara salanewa.
Don haka, ko don kanki uwargida ya kamata ki rika kula da zumarki, kada ki bari ta salance haka kuma kada a zugage ta da irin magungunan zamanin nan.
Mu sani, zaki ma in ya yi yawa daci yake zama, kuma zai sa ki zamo mai araha a wajen maigida.
Akwai hanyoyi da za ki bi don kula da zumarki ta kasance daidai-wa-daida kuma daidai da bukatar maigida.
Shawara ta gaba ga mai son zama mace daya tamkar hudu wajen mijinta ita ce; ya kamata mu rika kula da kanmu sosai bayan haihuwa, musamman haihuwar farko, in kika yi gyara mai kyau a haihuwar farko, to zuma da dandanonki za su yi karko sosai.
Shawara ta gaba son Allah, wato duk macen da ta cika zuciyarta da Allah, kuma so na hakika wanda babu algus a ciki, so gangariya ba na ganin ido ba, kuma so irin wanda canjawar yanayi da al’amura ba su canja shi, so irin wanda ba jin haushin Allah saboda wani ibtila’i ko jarrabawa ta rayuwa.
To irin wannan mata za ka tarar mijinta yana matukar son ta kuma yana jin gara ya rasa komai a kan ya rasa ta.
Da yawa muna yawan fadar muna son Allah amma ’yan kadan ne a cikin wadanda son da suke yi wa Allah na gaskiya ne.
’Yar uwa uwargida, bari in ba ki misalin masu son Allah na gaskiya don ki ji saukin yin amfani da wannan sirri wajen yin ganuwar karfe ga zuciyar mijinki.
Masu son Allah na gaskiya su ne suke yin aikin da ba su so, suna tsananin kyamar aikin nan, amma saboda umarnin Allah a kan wannan aikin sai su dage su yi ta yin sa, sannan wani abin kuma suna tsananin son aikata shi, domin suna jin dadin kuma yana kai su kololuwar jin dadin duniya, amma saboda hanin Allah a kan wannan, sai su guje shi su tursasa wa kansu aikata shi.
Kuma za su yi hakan zuciyarsu cike da ikhlasi, ba su jin ko sun yi wata jarumta ko sun yi wani abin a-zo-a-gani ba.
Sirri na gaba shi ne ki kula da jikinki, duk wani gyara da zai fito da kuma inganta arzikanki na ’ya mace to ki dabi’an ce shi.
Mace ta kan zama cikin jin dadi da nishadi marar misaltuwa in ya kasance kowane bangare na ’yan matancinta yana fitar da kyallinsa.
Sannan ki kula da shau’uka da tunane-tunanen da ke karakaina a cikin ma’aikatar hankalin ki, kada ki yarda bakin shauki da bakin tunani su yi tsiro balle har su girma su yi yado a cikin turbayar ma’aikatar hankalin ki, domin wadannan suna dusashe kyallin ’yan matanci da kuma samun natsuwar zuciya.
Kyallin ’yan matancin nan kuwa shi ne mafi girman abin da ke sa maza su rika kwawa da dokin matansu.
Komai kyan jiki da fuska, in ya kasance munanan shau’uka na karakaina a cikin zuciya, to kyan jikin zai zama bai da wata martaba balle tasiri mai kyau. Shawara ta karshe ita ce ki samar wa kanki kwarjini da cika ido a zuciyar mijinki.
Komai juyin juyahali kada ki taba bari kwarjininki ya dishashe.
Mace mai kwarjini maza ba sa iya rabuwa da ita kuma suna tsananin ganin darajarta.
Kula da kanki da noma kyawawan shau’uka cikin zuciya su ne tubalin ginin kwarjini.
Haka nan tsantsar son Allah shi ne bangon ginin kwarjini, sai kuma ba wa maigida dukkan hakkokinsa daidai iyawarki, shi ne mahadin da zai rike tubalin ginin, sannan in maigida ya shiga naki hakkin, ko ya taka martabarki ko mutuncinki, to cikin lumana da ruwan sanyi za ki taka masa birki ta yadda abin ba zai maimaita har ya zama dabi’a ba.
Sai mako na gaba in sha Allah. Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koyaushe, amin.
0 Comments