WASU ĎABI'U GUDA 10 DA SUKE MATUKAR KARBAR DUK WATA ĎIYA MACE WANDA YAKAMATA KOWACCE MACE TASANSU
(1) Shagwaba da kwantar da kai ga matar AURE ga mijinta (Kalar wacce ta karbe shi), da kuma rashin taurin kai da kafiya ga kowacce mace, ana son mace ta zamo me sauqin sarrafawa (A inda ya dace)✍.
(2)Son Ado, tsafta, qwalisa da qyale qyale (Ga waďanda ya dace).✍
(3)Rauni game da aikin Qarfi me wahala (Idan kika rasa wanda zai yi ki zage ki yi abin ki😥🥺) .✍
(4) Shigo da magabata masu hikima game da neman shawara kan duk wani Lamari ko hukunci da zata wanzar ko tunkara.✍
(5) Kamewa daga dukkan Namijin da ba muharraminta ba wanda wani mu'amalar Rayuwa ya hada shi da ita (kar ta zamo mara kunya gareshi, kar ta zamo me fitsara, kamar yi masa zancen Batsa, shigar tsiraici, ko qoqarin jefa shi Halaka da Aiki ko da magana) ta mu'malanci kowanne Namiji da mu'amala me tsafta idan Laluri ya gauraya rayuwarta da shi. Kar ta zamo fitina, ta zamo wacce ko da wani yaga zai mata abin da bai dace ba shi zai iya kareta, saboda yasan wacece ita.✍
(6) Yawaita Haquri: Duk yanda za ayi ana so mace ta kasance ba me tanka husuma bace ba, kar ta zamo me neman fitina, balle ace tana yawan fada da Al'umma, balle ace tana fada ko zage zage da Namiji.✍
(7) Son Ayyukan Cikin Gida: Ana so duk inda mace take asan cewa akwai mace tsayayya a cikin Gidan, wacce ta tsayu kan daidaita muhalli.✍
(8) Qaranta son abin Hannun mutane: Mace me yawan kwadayi musamman a inda bai dace ba bata cika daraja ba.✍
(9) Sauqar da Ido da bin gefen Hanya: kar ki zamo me qurawa mutane Ido, musamman Namiji, duk yanda za ayi ko kun hada Ido ki dauke na ki, amma kafa masa Ido bai dace da ke ba indai ba mallakin ki bane, to nan fa a mutu har Liman.✍
(10) Girmamawa: A miki shaidar Respect yafi miki Alkhairi akan ayi miki shaidar rashin girmama mutane, balle kuma ace kina da mugun Halinnan na qyamar mutane, da kinga wasu da basu dace da Ajin ki ko tsarin ki ba ki dinga guje musu bakya so su rabe ki, ke da zaki shiga Dangin wasu? Ko kina ma cikin su✍.
0 Comments