Wata sabuwa : Lakurawa sun hallaka Mutane da dama a Jihar birnin Kebbi
Rahotanni daga jihar Kebbi da ake arewa maso yammcin Najeriya sun ce aÆ™alla mutum 15 ne suka mutu a wajen wani artabu tsakanin mutanen gari da mayaÆ™an nan ‘yan kasashen waje da ake kira Lakurawa.
Lamarin dai ya faru ne a ranar Jumu’a a kusa da garin Mera na Karamar Hukumar Augie.
Jamilu Gulma wakilin jaridar Blueprint a jihar wanda ya bibiyi labarin ya shaida wa BBC cewa, wadansu makiyaye ne da suke kiwo a garin Mera, mutanen da ake sa ran ƴan Lukurawa ne suka ƙwace dabbobin.
“Sai makiyayin ya ruga da gudu ya shaidawa mutanen gari abin da ke faruwa, saboda haka matasan garin suka je aka yi artabu tsakanin su da mutanen a cikin jejin, inda aka kashe mutum 15 tare da jikkata wasu da dama.”
Jamilu Gulma ya ce mutanen garin sun yi nasarar kashe wasu daga cikin Æ´anbindigar, tare da jikkata wasu da dama, sai dai sun dauke mutanensu.
“Mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida, ya kai ziyarar jaje a garin na Mera tare da kwamishinan yansanda da sauran jami’an tsaro da mai martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera.”
BBC Hausa
0 Comments