GA WASU HADIN GARGAJIYA DAZA KIYI AMFANI DASU DON GYARAN NONO KAFIN BIKINKI HAR BAYAN BIKI.
1. Hadin Kara Lafiyar Nono (Don Santsi da Laushi)
Sinadaran:
Man zaitun (cokali 2)
Man kwakwa (cokali 2)
Zuma (cokali 1)
YADDA Ake AMFANI:
Ki hada wadannan sinadaran tare.
Ki shafa a nono ki dinga matsawa a hankali daga ƙasa zuwa sama na minti 10-15.
Ki bar shi na minti 20 sannan ki wanke da ruwan dumi.
Ana yin haka sau 3 a mako.
2. Hadin Cika Nono da Kiba
Sinadaran:
Dabino (5-7)
Madara (1 kofi)
Almonds (10)
Gyada (10)
YADDA Ake AMFANI:
Ki jika dabino da almonds da gyada a dare.
Da safe ki markada su ki sha da madara.
Ki dinga sha kullum na tsawon wata É—aya.
3. Hadin Tsukewar Nono (Don Matse Fata da Tsayar da Nono)
Sinadaran:
Farar kwai (1)
Ruwan lemon tsami (cokali 1)
Garin alkama (cokali 1)
YADDA Ake AMFANI:
Ki kwaba farar kwai da ruwan lemon tsami da garin alkama har ya yi laushi.
Ki shafa a nono ki bar shi na minti 15-20.
Ki wanke da ruwan dumi.
Ana yin hakan sau 3 a mako.
4. Hadin Goge Fatar Nono (Don Karin Haske da Dadi)
Sinadaran:
Kankana (yanka guda 1)
Man zaitun (cokali 1)
YADDA Ake AMFANI DASHI:
Ki markada kankana ki tace ruwan.
Ki hada da man zaitun ki shafa a nono.
Ki bar shi na minti 20 sannan ki wanke da ruwan dumi.
Ana yin haka sau 3 a mako.
0 Comments