HANYOYIN KARIYA DAGA CUTUTTUKA GUDA GOMA SHA BIYAR (15) WANDA YAKAMATA KOWA YASANI KUMA YA KIYAYESU
1- A tabbatar anyiwa yara rigakafi ( daga farawa har a gama ) domin karesu daga cututtuka.
2- Duk matar da ba'a yarda da tsaftar ta ba a kauracewa abincin ta .
3- A kiyaye tsabtar muhalli da ta bayan gida dan kada kuda su samu wurin zama .
4- A rufe duk wani abinci da abin sha da aka ci , don kada kuda ta hau.
5- Kada aci kayan Lambu Irin su salat wanda ba dafasu akeyi ba ,sai an wanke da ruwan manda .
6- A guji bayan gida barkatai a hanya da gefen magudanan ruwa ko rijiya ko kogi.
7- A tabbatar an tace sannan a tafasa ruwan da aka debo daga rafi ko rijiya kafin a sha .
8- A tabbata an wanke hannaye da sabulu bayan anyi bayan gida ko kuma anyiwa yara tsarki kafin cin abinci .
9- Kamewa daga jima'i har sai anyi Aure, kuma a tabbatar anyi gwaji kafin Aure.
10- Zuwa cibiyoyin gwaji lokoci bayan lokoci domin mutum yasan matsayin sa yakan taimaka wajen rage yada cututtuka.
11- Idan mutum bazai iya kamewa daga jima'i har zuwa bayan Aure ba , a tabbatar anyi amfanu da kororon roba lokocin jima'i.
12- Zuwa uwan mata masu juna biyu , yakan taumaka wajen kare cututtuka da dama.
13- A rage shan magani barkatai babu gaira babu dalili , a tabbatar kafin asha magani sai da izinin likita.
14- Kada ayi wasa da lafiyayyen abinci , domin abinci shi yake gina jiki da garkuwa jiki.
15- A tabbatar ana kwana a gidan sauro , domin kwanciya a gidan sauro yakan kare ka daga kwari masu cutar wa su sameka.
0 Comments